Kungiyar Kwallon kafa ta Wikki Tourists sun kulla kwantiragi da dan wasan kasar Masar dan shekaru 24 mai suna Mahmud Gamal kan kudin da ba abayyana ba, har na tsawon kakan wasanni na shekaru 2020/2021 da Kuma 2021/2022
Mahmud Gamal Wanda hukumar gudanarwar ta kungiyar Wikki ta bayyana shi a idon yan’jarida masu rubutun labarin wassanni a zauren dakin wassani na Jihar, a ranar Litinin, inda dan wasan ya rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar buga ma kungiyar wasan kwallon kafa
Jim kadan bayan ya rattaba hannu kan takardar, sai mai mashi jagoranci, Philip Dosu, yace sun yanke hukuncin dan wasa ne, da ya zo ya buga gasar tamola a kasan Najeriya, tunda kungiyar ta nuna sha’awarta na dauko shi, don ci gaba da zagaye na biyu na kakar bana a Najeriya.
Kana Philip Dosu ya kada baki yace, kungiyar kwallon kafan mallakar Jihar Bauchi, Wiikki Tourist, baza tayi nadamar sayen dan wasa Mahmud Gamal ba,
inda zai gwada bajintarsa yayin da aka dawo buga gasar kwararrun na Najeriyar a tara 9 ga watan gobe na Mayu
Ana shi jawabin dan wasan wanda mai tare farmaki ne ta gefen hagu, yace yayi farin ciki zuwanshi Najeriya kuma kungiyar kwallon kafa ta Wikki, inda zai nuna gogewarsa, yace bazai ba mara da kunya ba, ya kara da cewa ya baro tsohuwar kungiyar sa ne (Egypt Insurance FC) kuma an bayyana cewa shi kwarrarene wajen bugun daga kai sai ma tsaron raga
Har ila yau, kungiyar ta sayo zakakuran Yan’wasa guda hudu daga kungiyoyi na cikin Najeriya don zage damtse, da sake dammara don Kar kungiyar ta bawa mara da kunya a kakar wasan ta bana, Wanda rashen katabus ya jima yana yima magoya bayan Wikkin turnuki a cikin zukatansu tare da rashin tabbas ga yan’wasan kungiyar.
Bugu da kari, magoya bayan Wikkin kuwa sun nuna goyan baya da chanjin da aka samu na sabbin Yan’wasa, ko hakkarsu zata cimma ruwa a zagaye na biyu na gasar.
Daga Adamu Shehu Bauchi