Bataliyar Wike Ta Janye Daga Rundunar Yakin Atiku

Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar 2023 ta afka cikin ruɗani, yayin da bataliyar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ke jagoranta ta janye jiki daga shiga yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ɗin.

Wannan janyewar da su ka yi ta zo ne daidai saura mako ɗaya a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta bayar da iznin fara fafatawa daga ranar 28 ga Satumba.

Sanarwar ta fito ne daga bakin ɗaya daga cikin zaratan Wike, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Olabode George.

Bode George ya yi sanarwar bayan sun kwashe tsawon ranar Talata zuwa washegarin Laraba su na ganawar sirri a gidan Gwamna Wike da Fatakwal.

Daga cikin mayaƙan da su ka halarci taron janyewa daga rundunar Atiku 2023, akwai Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Olabode George, tsoffin gwamnoni irin su Segun Mimiko, Ayo Fayose, Donald Duke, Ibrahim Ɗanƙwambo, Jonah Jang da tsohon Ministan Shari’a, Mohammed Adoke.

Akwai kuma tsohon Minista Jerry Gana da Shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu, Dan Orbih, sai tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Chibudom Nwuche da wasu hamshaƙan PDP da dama.

Ɓangaren Wike ya ce ba zai shiga kamfen ɗin Atiku ha har sai Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙamin sa, an naɗa ɗan Kudu, domin a yi adalcin raba-daidai.

Wani jigon PDP dai ya ce tun farko Ayu ne janyo saɓani da Wike, domin bai kamata ya gidan gidan Tambuwal yin godiyar haɗa-bakin yin nasarar Atiku a zaɓen-fidda-gwani ba.

Wani jigon PDP kuma fitaccen lauya, Obunike Ohaegbu, ya bayyana cewa a gaskiya tun farko dai Shugaban PDP Iyorchia Ayu, ya tafka kuskure da ya je har gida ya yi wa Gwamna Aminu Tambuwal godiyar haɗa kai da ya yi da Atiku Abubakar aka kayar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a zaɓen fidda gwani.

Ohaegbu ya bayyana wannan ra’ayi na sa a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na AIT, a ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, bayan Atiku ya yi nasarar kayar da sauran ‘yan takara, Shugaban PDP Ayu ya samu Tambuwal har Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto washegari, inda ya yi masa godiya, saboda ya ce dukkan magoya bayan sa su zaɓi Atiku.

An yi ittifaƙin cewa janyewar da Tambuwal ya yi ce ta sa Atiku ya samu yawan ƙuri’un da ya kayar da Wike.

Tun daga nan kuma Wike ya riƙa kiran su Tambuwal da Ayu maciya amana.

Labarai Makamanta

Leave a Reply