Basussukan Da Gwamnati Ta Karbo Sun Taimaka Ga Manyan Ayyuka – Mohammed

An bayyana cewar tarin basussuka da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari ke karɓowa daga ƙasashen waje sun taimaka matuƙa wajen aiwatar da manyan ayyuka a faɗin ƙasar nan.

Ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar gani da ido dangane da aikin hanyar jirgin kasa da ake yi wacce ta taso daga Legas zuwa Ibadan zuwa Kano.

Ministan ya cigaba da cewar babu wata illa akan karbar rance muddin za’a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa.
“A fili yake gwamnatin Buhari ta yi rawar gani wajen inganta rayuwar al’ummar Najeriya, kuma abu ne da kowa ya gani mun yi abubuwa na raya ƙasa fiye da gwamnatocin da suka gabace mu”.

Lokacin da yake nashi jawabin Ministan sufuri Mista Rotimi Amaechi, yace Najeriya na bukatar Dala Biliyan biyar da rabi wajen kammala aikin hanyar titin dogon, sannan ya yi kira ga majalisar tarayya da ta amince da shirin ƙarbo bashi dags ƙasar Chana domin tasirin da hakan yake dashi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply