Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Tiriliyan 121 – Hukumar Kula Da Basussuka Ta Kasa

IMG 20240429 WA0024(1)

Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa (DMO) ya bayyana cewa ƙididdigar basussukan da ake bin Najeriya zuwa watan Maris ya kai Naira tiriliyan 121.67, watau kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 91.46 kenan.

Babban Daraktan Hukumar DMO, Patience Oniha ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwar da ta fitar a Abuja.

Oniha ta ce wannan tulin bashi ya haɗa da wanda ake bin gwamnatin tarayya da kuma jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.

Ta ce zuwa watan Maris, adadin basussukan cikin gida da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 65.65, yayin da basussuka na waje sun kai Naira tiriliyan 56.02.

Ta ƙara bayyana cewa bashin ya ƙaru ne sosai saboda basussukan cikin gida da aka ciwo domin cike giɓin kasafin 2024, sai kuma tashin gwauron zabin da Dala ta riƙa yi, I a kuma Naira darajar ta na karyewar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply