Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Naira Tiriliyan 31 – Hukumar Kula Da Basussuka

A ranar Laraba, ofishin kula da basussukan Nijeriya (DMO), ya wallafa N31.009trn ko kuma $85.897, a matsayin bashin da ake bin kasar, ya zuwa ranar 31 ga watan Yuni, 2020.

Hakan na nufin cewa bashin da ake bin kasar ya karu da kaso 8.3, daga N28.628trn a watan Maris 2020 zuwa N31.009trn a watan Yuni, 2020.

Adadin kudin ya shafi bashin da ake bin gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja (FCT).

Ofishin DMO, a cikin rahoton da ya saki ranar Talata, ya bayyana cewa, “Karin bashin da N2.3trn ko USD6.593 ya faru ne sakamakon wasu dalilai kamar haka.
“Na farko bashin dala 3.36bn da aka ciyo don tallafawa kasafin kudin 2020 daga asusun bada rance kudi ga kasashe, sai kuma bashin da aka ciwo na cikin gida a kasafin kudin 2020.

“A cikin bashin da aka ciwo na cikin gidane aka ware N162.557bn na Sukuk, da kuma kudaden da aka ware na biyan hakkokin masu shigo da kaya cikin kasar.”

Ofishin DMO ya kuma ce za a iya samun karin kudaden idan har aka ce kudaden da ake da su a kasa ba zasu isa kammala kasafin wannan shekarar ba, dole a ciwo wani bashin.

“Ofishin DMO na sa ran bashin da ake bin Nijeriya zai karu, da zaran an kara ciwo bashi a cikin gida daga babban bankin duniya, bankin bunkasa Afrika, da kuma bankin Musulunci na IDB, wanda ake sa ran zasu bada rance don kasafin 2020.

“Ya zama wajibi a sabunta dokar kasafin 2020 la’akari da barnar da COVID-19 ta yiwa tattalin arzikin gwamnati da kuma kara kudaden da aka kashe a fannin kiwon lafiya.

A farkon makon nan ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta rasa kaso 60 na kudaden da take hasashen samu sakamakon barkewar annobar COVID-19. Hakan ya jawo babban cikas ga tattalin arzikin kasar da ma duniya baki daya, da kuma tilasta karyewar farashin danyen mai, hakan zai tilasta kasar ta ciwo basussuka.

An ruwaito cewa, akwai jiragen Nijeriya makare da danyen mai a cikin tekuna ba tare da samun mai saye ba, sakamakon mafi yawan kasashe an rufe su saboda tsoron yaduwar COVID-19.

Labarai Makamanta