Barka Da Sallah: Shugaban Kasa Ya Bukaci Musulmi Su Sanya Najeriya Cikin Addu’a

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sako na musamman yayin da al’ummar Musulmi ke shirin fara hidimar babbar sallah. Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga Musulmi kan sadaukarwa domin kowo nasara da cigaban ƙasa.

A cikin wani sako da jami’in yada labaran fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nuni da cewa babbar sallah tana da alaƙa da sadaukarwa ne da aka yi a baya. Saboda haka ya buƙaci yan Najeriya da su nuna sadaukarwa domin ta hanyar haka ne kawai za a gina kasa mai inganci.

Haka zalika Tinubu ya mika godiya kan sadaukarwa da juriya da yan kasa suka nuna cikin shekara daya da ya yi yana gyaran Najeriya.

Tinubu ya ce Najeriya na bukatar addu’a Bola Tinubu ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi kokarin yin adduo’i na musamman ga kasar a wannan lokaci mai albarka.

Shugaban kasar ya ce a hakikanin gaskiya Najeriya na buƙatar adduo’i domin samun zaman lafiya da cigaba.

‘Ba zan ba ku kunya ba’ Dangane da halin da ake ciki na matsin rayuwa, Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta fara daukan saiti kuma ana daf da cin nasara.

Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba domin yana kokarin tabbatar da ya cika alkawuran da ya yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply