Barazanar Yajin Aiki: Ministan Ilimi Ya Gayyaci Malaman Jami’o’i

Biyo bayan barazanar sake tsunduma yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ta kuduri aniyar yi, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya gayyaci shugabannin kungiyar malaman jami’o’in (ASUU), zuwa wani taron gaggawa domin lalubo bakin zaren.

Taron wanda aka shirya yi a ranar yau Talata 06/04/21 yana zuwa ne bayan barazanar da kungiyar Malaman Jami’o’in ta yi na shiga wani yajin aikin.

Bayanin hakan ya faru ne a yammacin Litinin yayin da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Bem Goong, ya ruwaito Ministan yana bayanin cewa taron “an shirya shi ne domin yajin aikin dake tafe.”

Sanarwar ta ce: “Ministan Ilimi Adamu Adamu ya gayyaci kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) taron gaggawa bayan barazanar shiga wani yajin aikin.

“Taron gaggawa zai gudana ne a ranar Talata 6 ga watan Afrilu 2021 da karfe 11:00 na safe a Hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.

“Da yake bayanin dalilin taron na gaggawa, Ministan ya ce taron na da niyyar kare tsundumawa yajin aikin ne da ke tafe.

“Za a tuna cewa ASUU ta fitar da sanarwar yajin aiki a kan abin da kungiyar kwadagon ta bayyana a matsayin kin Gwamnati na aiwatar da wasu yarjejeniyoyi da aka kulla tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarayya.

“ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi a watan Janairun bana.”

Related posts

Leave a Comment