Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Bankuna da asusun ajiya za su bukaci KYC daga jama’a ko kuwa a rufe masu akawun saboda rashin NIN/BVN KYC shi ne tsarin da banki yake bi domin samun muhimman bayanan da ake bukata daga duk abokin huldarsa.
Babban Bankin Ƙasa CBN ya bada umarnin a rufe asusun da aka samu bai da lambobin banki na BVN ko NIN ta shaidar zama ‘dan Najeriya.
Asusu sama da miliyan 70 suke cikin barazana a yau a sakamakon umarnin da bankin CBN ya ba bankunan kasuwa. Babban bankin Najeriya na CBN ya bada umarni a rufe asusun da bai da lambobin BVN da NIN daga farkon Maris na 2024.
Idan aka aiwatar da wannan umarni, rahoton Leadership ya ce akwai asusu kimanin miliyan 85 wadanda ba su cika sharudan ba.
Da zarar an toshe akawun, abokin huldar banki bai da damar da zai cire kudi ko ta wani irin hali ko kuwa ya aika wani asusun.
Umarnin da CBN ya bada ta ofishin darektocinsa, Chibuzo Efobi da Haruna Mustapha sun wajaba alakanta asusu da BVN da NIN.
Ana bukatar NIN da BVN a kananan asusu?
Kamar yadda Legit ta fahimta, dokar ta shafi kananan asusun ajiya irinsu Opay da kuma manyan bankunan kasuwanci na kasar. An gargadi bankuna cewa bayan bincike, za a hukunta wadanda suka sabawa umarnin CBN, don haka aka fito da hanyoyi.
Wannan ya jawo bankuna suka rika bada dama daga manhajojinsu domin masu hulda da su su gabatar da lambobin da ake nema.
Shugaban ‘yan POS ya roki CBN Punch ta ce shugaban kungiyar masu harkar POS, Sarafadeen Fasasi, ya roki bankin CBN ya kara wa’adi domin kammala aikin KYC.
Sarafadeen Fasasi ya ce kamar yadda alkaluma suka nuna a lokacin da ake yin rajistar BVN, za a iya rufe asusu miliyan 70 a bankuna. Mutane kimanin miliyan 104 suke da NIN a cikin mutum miliyan 200, don haka ake ganin akwai bukatar a ba bankuna karin lokaci.