Bankuna Na Da Hannu Dumu-Dumu Wajen Rusa Arzikin Najeriya – EFCC

images 2024 03 06T065548.413

Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, A Ranar Litinin, ta tuhumi bankuna da alaƙa da kusan kashi 70 na Tabarbarewar Tattalin arziki a Najeriya.

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukayode, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a Abuja a wajen taron shekara-shekara Da babban taron Kungiyar manyan Masu binciken kuɗi na bankuna a Najeriya.

Yayi nuni da cewa, harkar banki na kara zama wata hanyar damfara kuma hakan na kara jawo kalubale da damuwa ga tattalin arzikin Najeriya.

Olukayode Wanda Ya samu wakilcin Darakta a Hukumar ta EFCC, Idowu Apejoye, Yace akwai buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe daga hukumomin da abin ya shafa, Musamman masu Gudanar da bincike domin dakile da kuma magance matsalolin da suka shafi zamba a fannin bankuna.

Olukayode ya bayyana cewa, domin dakile matsalar, ya kamata ACAEBIN ta tabbatar da daidaita asusu a duk wata kamar yadda ake bukata.

Ya kuma umarci kungiyar da ta sanya ido kan harkokin kudi na bankuna.

Shugaban kungiyar, ACAEBIN, Prince Akamadu, ya ce kungiyar za ta yi kokarin cimma wasu shawarwarin da shugaban EFCC ya bayar.

Ya kuma bayyana cewa kungiyar ta dukufa wajen ganin an Gyara kalubalen canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a Najeriya, wanda yana daya daga cikin batutuwan da jajircewar tayi niyyar cimmawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply