Bani Da Matsala Da Ƙasar Amurka – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce shi da iyalansa ba su aikata wani laifi ba saboda haka ba su cikin wadanda Amurka ke sanya wa ido ko bincika.

Akwai wani rahoto da aka wallafa da ke cewa Cibiyar Hana Laifukan Kudi, FINCEN da ke karkashin Sashin Kula da Baitul Malin Amurka tana saka ido a kan Atiku da wasu cikin iyalansa.

Amma cikin martanin da ya yi a ranar Talata, Kakakin Atiku, Paul Ibe ya ce: “Wannan tsohon zargi ne mara tushe da aka dade ana yinsa.”
Ya ce an wallafa rahoton ne domin karkatar da hankalin ‘yan Najeriya daga sanarwar da sakataren Amurka, Mike Pompeo ya fitar a baya bayan nan kan haramtawa wasu ‘yan Najeriya shiga Amurka saboda magudin zabe.

“Idan ba a manta ba an wallafa wannan karerayin gabanin zaben shugaban kasa na Fabrairun 2019.

Mai girma Atiku Abubakar ya nemi izinin zuwa Amurka kuma an bashi, ya tafi a ranar 17 ga watan Janairun 2019.

“Ya sauka a wani otel da ke kusa da Hukumar Shari’a ta Amurka. “A yayin ziyarar, wasu jami’an gwamnatin Amurka sun gana da shi. “Ganin cewa an fitar da wannan rahoton kasa da awa 24 bayan zaben gwamnan jihar Edo shima abin tambaya ne da ya dace mutane suyi la’akari da shi.

“Ina son tunatar da al’umma cewa Atiku da iyalansa suna kasuwanci mai tsafta ne bisa dokokin Najeriya da na kasashen waje,” in ji shi.

A cewar rahoton da Premium Times ta wallafa, sabbin bayanai sun nuna cewa FINCEN tana bincike a kan wasu hada-hadan kudi da ke da alaka da babban dan siyasan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply