Bani Da Hutu Sai Naga Bayan ‘Yan Bindiga A Kasar Nan – Shugaban Dakarun Soji

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban dakarun sojin kasa, Janar Faruk Yahaya ya ja kunnen cewa ba zai lamunci uziri daga kwamandojin da ke jagorantar dakarun soji ba a filin daga da kuma yakar matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba.

Yahaya ya bada wannan wannan jan kunnen a yayin bude wani taro kashi na biyu da na uku na sojin da aka hade a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.

Ya ce rundunar da ke karkashinsa za ta cigaba da mayar da hankali tare da kokarin ganin ana samun cigaba wurin yakar matsalolin da ake ciki, domin kakkabe ragowar ‘yan bindiga da suka yi saura.

Shugaban dakarun sojin ya bayyana cewa ya umarci dukkan sojoji da ke ayyukan samar da zaman lafiya da su cigaba da aikin da suke yi tare da karawa, domin cimma muradun rundunar na shafe tarihin ‘yan Bindiga a kasar.

Ya kara da cewa, ya umarci dukkan dakarun dake ayyukan da na musamman da jajirjewa ballantana a yankin arewa ta tsakiya da arewa maso yamma da su cigaba domin shawo kan matsalar tsaron yankunan.

“A don haka, dole ne kwamandoji su tabbatar da sun cigaba da ayyukansu tare da cigaba da tsananta su har sai an cimma manufa. “Dole ne kwamandoji su fito da dabaru kuma mabiyansu su dauka, dole ne a dauka mataki cin galaba kan dukkan kalubale ba tare da duban yankunan ba.

Related posts

Leave a Comment