Jigo a Jam’iyyar APC kuma makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari sannan tsohon dan majalisar tarayya, Farouk Adamu Aliyu, ya tabbatar da cewa mutanen Najeriya sun fada cikin matsanancin hali a kasar nan a wannan lokaci na mulkin Buhari.
Da ya ke tattaunawa da BBC Hausa, Farouk Aliyu ya ce” Ni ma na shekara 60 a duniya yanzu amma ban taba ganin an shiga matsi irin haka ba.
Sai dai kuma Ɗan siyasan ya ce an samu cigaba da dama a kasa Najeriya duk da matsin da aka shiga.