Ban Cire Tsammanin Zama Shugaban Ƙasa A 2023 Ba Tinubu

Jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tnubu ya faiyacewa ‘yan uwansa Yarbawa, tare da manema labarai a babban dakin taron su dake Leges, bayan kammala wata zama da suka yi.

Zaman ya hada da manyan ‘yan majalisun kasar Yarbawa, tare da ‘yan kasuwansu, wadanda su kayi fice a kasashen Turai.

Kazalika an shirya zaman ne domin fitar da dabarun bibiyar wadansu hanyoyi mafi sauki domin cimma manufar Yarbawan na ganin an samar Tinubu takardar shedar tsayawa takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2023 dake zuwa.

Jiga-jigan ‘yan majalisu magoya bayan hakan sun rattaba hannaye, tare da gamsuwa da irin wannan salon da za su bi, domin ganin sun kai ga nasarar tabbatar da Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasar Nijeriya a nan gaba.

Bayan haka kwamitin gudanar da zaman sun dauki aniyar batar da makudan kudade bisa kan wannan tafarkin.

Mene ne ra’ayoyin ku masu karatu??

Labarai Makamanta

Leave a Reply