Iyalan dan kasuwar nan dan asalin jihar Katsina, mai kwarmato kan gwamnatin jihar Katsina Mahadi Shehu, sun bayyana fargaba kan halin da mai gidan nasu ke ciki tun bayan da ‘yan sanda suka kama shi a makon jiya.
Gwamnatin jihar Katsina ce dai ke zargin Mahadi da buga bayanan bogi da yin kalaman ?ata suna ga gwamnatin da jami’anta, inda shi kuma yake zargin ta da barnatar da biliyan ?52.6bn na asusun tsaron jihar, a cikin shekara biyar.
Wani daga cikin iyalan gidan Mahadi, ya shaida wa Daily Trust a ranar Talata cewa rabon da su ji ?uriyar halin da yake ciki tun lokacin da aka ce maciji ya sare shi a harabar shelkwatar ‘yan sanda da ke garki Abuja, yana mai cewa su yanzu ba su da tabbacin Mahadi na raye ko a mace, tare da nuna rashin gamsuwarsu kan yadda ?ansandan ke ci gaba da tsare shi.
Kokarin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan Frank Mba da Daily Trust ta yi ya ci tura, saboda bai dauki waya ba, kuma bai bada amsa ga sakon da aka tura masa ba.