Shugaban dakarun sojin saman Najeriya, Sadique Abubakar, ya ce dakarun rundunarsa za su ci gaba da yakar ‘yan bindiga har sai ‘yan kasa na iya fita su yi harkokinsu babu fargaba.
Abubakar ya bayar da wannan tabbacin ne yayin bude wasu dakuna 20 da aka gina wa dakarun a ranar Laraba a Birnin Gwari ta jihar Kaduna, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.
“Dole ne mu ci gaba da yaki a kasar nan har sai ‘yan kasa na iya fita babu takura ko fargaba.
“Wajibi ne a garemu da mu sauke nauyin da ke kanmu cike da kwarewa don kare kasar mu daga ‘yan ta’adda da tsageru,” cewar shugaban.
Kamar yadda Abubakar yace, hakan suna yin shi ne don cimma tsarin NAF da kuma cike rantsuwar aiki da suka yi.
Abubakar ya ce akwai bukatar a duba babban aikin da dakarun ke yi a Birnin Gwari wurin shawo kan manyan kalubalen tsaro da suka addabi yankin.
Ya kara da cewa, hukumar za ta ci gaba da samar da kayayyakin bukata da za su bai wa jami’an kwanciyar hankali don yi aikin su yadda ya dace.
“Ba sai an fadi ba, tsaron sama da soji ke yi tare da kai dauki a jihohin Niger, Kaduna, Zamfara, Katsina da Sokoto suna matukar yin amfani.
“Amma kuma, wannan ba lokacin yada makamai bane. Ina farin cikin sanin cewa wadannan dakarun sun halaka wasu ‘yan bindiga a ranar 7 ga watan Yuli a yayin da suke sauke hakkinsu,” yace.
Shugaban rundunar sojin saman ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kan goyon bayan da yake bai wa NAF wanda hakan yasa suke iya sauke nauyin da ke kansu.
Ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa dakarun sun mayar da hankali wurin tabbatar da samar da Najeriya mai cike da zaman lafiya.
A ci gaban tabbatar da kawo zaman lafiya da dakarun sojin Najeriya ke yi, rundunar Operation Hadarin Daji karkashin Operation Accord a ranar 7 ga watan Yulin 2020, ta hadu da ‘yan bindiga a karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto.
A yayin amfani da salon iya yaki, dakarun sunyi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda suka kashe biyu daga ciki. Wasu daga ciki sun tsere da raunika sakamakon harbin bindiga.
Hakazalika, a ranar 8 ga watan Yuli 2020, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri a kan kaiwa da kawowar ‘yan bindigogi masu tarin yawa. Sun tsaresu a yayin da suke tafiya da shanun sata zuwa kauyen Jangemi da ke kusa da garin Kwaren Ganuwa.