Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata labarin boye kayan abincin tallafin COVID-19 da kungiyoyi masu zaman kansu suka samar don sassautawa talakawa radadin zaman gida lokacin kullen COVID-19.
Kungiyar manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka taru suka kira kansu da CACOVID, sun hada biliyoyin nairori don taimakon ‘yan Najeriya a kan cutar Coronavirus, wacce tayi ajalin mutane a kalla 1,139, sannan ta shafi mutane 62,992.
A cikin kudaden da suka hada an yi amfani da wasu don gina cibiyoyin kula da lafiya da magunguna cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja. Yayin da aka yi amfani da wani bangare na kudin don siyan kayan abinci don rabawa talakawan da ke fama da yunwa yayin zaman gida.
Bayan an bayar da kayan abincin ne gwamnatin jihohi suka killace su a ma’adanar su, suna tunanin yadda za su raba kayan abincin. Bayan zanga-zangar EndSARS ne wasu bata-gari suka nemo adireshin ma’adanar da ke jihohi, suka shiga suka kwashe su tas, a jihohi kamar Legas, Osun, Taraba, Kaduna da sauransu.
Kamar yadda aka sani, Legas babban birni ne inda ake ajiye-ajiyen kayan amfani, ba kayan tallafin COVID-19 kadai ba. Yanzu haka a cewar wasu jihohin, sun adana kayan tallafin ne idan guguwar COVID-19 ta biyu ta tashi, sai a rabawa talakawa.
Kungiyar gwamnonin Najeriya tace ya kamata gwamnoni su gyara yadda suke tafiyar da mulkinsu don kawo gyara, suyi iyakar kokarin su don ganin ba su yi abubuwan da za’ayi musu mummunar fassara ba.
?ungiyar Gwamnonin na iyakar kokarin ganin ta tabbatar da adalci da mulki mai inganci a Najeriya.