Bama Goyon Bayan Buɗe Makarantu Yanzu – Gwamnatin Tarayya

A yayin da ake shirin bude makarantu domin cigaba da gabatar da al’amura kamar yadda ya kamata a jihar Legas da wasu jihohi na Najeriya, kwamitin gudanarwa ta fadar shugaban kasa ta gargadi masu ruwa da tsaki wajen bude makarantun.

Sakataren gwamnatin tarayya, sannan kuma shugaban kwamitin gudanarwa na fadar shugaban kasa, Boss Mustapha, ya bayyana abinda ya faru a kasashen waje bayan bude makarantu.

Mustapha ya sanar da cewa hakan shine mafita ga Najeriya abi dokar da aka sanya tun farko.Ya ce: “Akan haka ne kwamitin gudanarwa take magana akan bude makarantu da mutane ke ta kira ayi, yayin da wasu ma tuni sun fara shirye-shiryen bude makarantun.

“Duk da kwamitin gudanarwar bata hana gabatar da wannan shirye-shirye ba, amma ya kamata muyi duba da abinda ya faru da kasar Jamus, Faransa, da kasar Amurka, inda bude makarantu a wasu biranen ya jawo karuwar yaduwar cutar da kuma mace-mace.

Haka kuma ya ce kwanan nan za a bude wasu daga cikin ma’aikatu, musamman ma a yanzu da kasar za ta shiga yanayi na cire dokar hana zirga-zirga.Mustapha ya ce kwamitinsu za ta mika abinda take ganin ya kamata ayi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin wannan makon, inda hakan shine zai bayar da abinda ya kamata ayi nan gaba.

Ya bayyana cewa makonni uku da suka gabata an samu raguwar yaduwar cutar a Najeriya, inda yacecikin watanni hudu da aka yi, a ranar 30 ga watan Agusta ne aka fi samun raguwar mutanen da suka kamu, inda aka samu mutum 138 kacal.Shugaban kwamitin ya kuma yi gargadi akan mutane su lura sosai, saboda har yanzu cutar tana nan tana yawo a cikin al’umma.

Labarai Makamanta

Leave a Reply