Badakalar Tiriliyan Hudu: Sanatocin Arewa Sun Koka Bisa Zargin Da Ake Wa Shugaban Majalisa

IMG 20240310 WA0183

Sanatocin Arewa sun bayyana damuwarsu game da badakalar kasafin kudin da ake zargin Akpabio Kimanin Tiriliyan huɗu.

Sanatoci daga yankin Arewa na kara nuna damuwarsu kan yadda Akpabio da mukarrabansa suka sanya ayyukan inganta kansu da suka kai Naira tiriliyan hudu a cikin kasafin kudin ta hanyar da bata dace ba.

Mambobin kungiyar mai wakilai 58 ƙarƙashin jagorancin Abdul Ningi (PDP, Bauchi) sun tattauna a Ranar Alhamis a Gidan baki da ke gundumar Maitama a Abuja.

A yayin hirarsa da Sashen Hausa na BBC, Abdul Ningi ya tabbatar da cewa akwai kasafin kudin tarayya daban-daban guda biyu da ake aiwatarwa.

Yace, “A cikin watanni uku da suka Gabata, mun dauki masu binciken kudi masu zaman kansu don yin nazari sosai kan kasafin kudin 2024. Mun gano manyan sauye-sauye da kari ba tare da izini ba a cikin kasafin kudin da zai yi mummunar tasiri ga ƙasa baki daya.

“Ya kamata mu gana da Shugaban majalisar dattawan mu nuna masa kura-kurai da muka gani a cikin kasafin kudin mu sanar da shi damuwarmu. Ba za mu yarda mu goyi bayan kashe kuɗi akan abin da ba mu sani ba. Baya ga kasafin kudin da Majalisar Dokoki ta kasa tayi, wasu sun bi bayanmu sun shirya wani kasafin kudin da ba mu sani ba. Akwai abubuwan da ba mu sani ba, amma masananmu har yanzu suna aiki a kai.

“Misali, Mun yi kasafin Naira Tiriliyan 28, amma bayan da muka yi cikakken bincike, mun gano cewa kasafin Naira Tiriliyan 25 ne. Ta yaya kuma a ina muka samu karin Naira tiriliyan 3,?

“Kuma akwai wasu batutuwa da yawa da muka gano. Za mu gana da shugaban kasa mu nuna masa; zamu tambaye shi ko yana sane da duk waɗannan abubuwan dake faruwa? Zamu nuna masa kuma mu tambaye shi ko yana sane da abin da akayi

Labarai Makamanta

Leave a Reply