Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Badakalar Biliyan 80: EFCC Ta Damke Akanta Janar Na Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar ya?i da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar na tarayya bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.

Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook inda ta ce ta kama shi a ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.

Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da ku?in ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.

EFCC ta ce an yi amfani da ku?in wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.

An kama Idris bayan ya ?i kar?ar gayyatar da EFCC ta rin?a aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Exit mobile version