Ɗan Majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar birnin Zariya Honorabul Mahmud Lawal, ya bayyana matakin da tsohon gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufa’i ya ɗauka na zuwa kotu kan binciken da ake yi mishi a matsayin abin dariya kuma shure-shure ne da ba zai hana mutuwa ba.
Honorabul Mahmud Lawal wanda aka fi sani da suna Bola Ige ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da ya yi da wakilinmu a Kaduna.
Honorabul Lawal wanda yana ɗaya daga cikin ‘ya’yan kwamitin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa domin bincikar badaƙalar El-Rufa’i, ya ƙara da cewar abin mamaki ne matuƙa zuwan El-Rufa’i Kotu, bayan kasancewar shi a baya mutumin da ya yi fice wajen rashin ganin girman kotu.
“Abin da ya kamata El-Rufa’i ya sani shine, tsarin ƙasa na tafiya ne bisa marafu huɗu wato bangaren zartawa da majalisa da kuma ɓangaren Shari’a, kuma kowane bangaren ba ya shiga hurumin ɗan uwansa, to zuwan El-Rufa’i Kotu yana nufin zai hana bangaren majalisa gudanar da aikin su ne? Ina tabbatar muku El-Rufa’i zai gane kurensa, kuma bada dadewa ba jama’a za su shaida haka”.
Bola Ige ya ce yana mai takaicin sanar da jama’a cewa a tarihin gwamnatin Jihar Kaduna ba a taba yin gwamnati wadda ta yi facaka da dukiyar al’umma cikin rashin imani kamar ta El-Rufai ba, adadin makudan kudaden da El Rufai ya ce ya fitar domin gudanar da ayyuka ba a kashe ɗaya cikin kashin biyar na kuɗin ba, aka karkatar da su ta wani bangaren daban.
“Zan ba ka misali da abin da ya faru a Zariya Kofar doka an ce an fitar miliyoyin kuɗi domin gudanar da aikin hanya, an yi amfani da Bul-Doza an rusa wa jama’a wurin zama shikenan an tafi an barsu cikin wannan radadi ba su ga tsuntsu ba su ga tarko”.
“Dukkannin ayyukan da El-Rufa’i ya yi a Kaduna ayyuka ne na cuwa cuwa marasa inganci, ka duba hanyoyin cikin gari wanda aka yi ta unguwar Dosa zuwa Malali tuni duk sun tabarbare, ka duba aikin da aka yi na ginin kasuwar magani, tun kafin akai ga an shiga abubuwa sun lalace! Mafi cin amanar da aka yi shine batun yin aikin hanyar titin jirgi cikin gari an ware miliyoyin kuɗi domin wannan aikin, amma daga bisani babu abin da aka yi akai, sannan babu kuɗi ba labarinsu, sai cewa aka yi a rubuce wai an kashe wadannan kuɗaɗe ne wajen zanen taswira”
Ɗan Majalisar ya bayyana cewar kudaden da El-Rufa’i ya yi watanda dasu da sunan aikin wanda sun zarce Biliyan 432, ba abu ne da za a lamunta ba, dukiyar jama’ar jihar Kaduna ce kuma dole a karbo musu hakkin su daga maciya amanar jihar.
Daga ƙarshe Honorabul Mahmud Lawal ya bukaci jama’ar Jihar Kaduna da su sa kwamitin binciken nasu cikin addu’o’i, domin samun kai wa ga nasara na wannan gagarumin aiki da aka ɗora musu alhakin sa.