Badaƙalar NDDC: Akpabio Ya Fallasa Sunayen Wasu Gwamnoni

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio ya alakanta wasu tsoffin gwamnoni uku da wasu ayyukan kwangiloli da hukumar ci gaban Neja Delta (NDD) ta bayar.

A cewar jaridar The Sun, Akpabio ya yi zargin cewa gwamnoni biyu daga jihar Delta sun aiwatar da wasu kwangilolin hukumar.

An kuma tattaro cewa ministan ya ambaci sunan tsohon gwamnan Abia a matsayin wanda ya amfana daga kwangilolin.

Jaridar ta bayyana cewa sunayen da Akpabio ya ambata a cikin jawabin sun hada da:

  1. Emmanuel Uduaghan (tsohon gwamnan jihar Delta)
  2. James Ibori (tsohon gwamnan jihar Delta)
  3. Sanata Uzor Kalu (tsohon gwamnan jihar Abia)
  4. Sanata Ifeanyi Ararume

Sai dai kuma a martaninsa Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia wanda ya ke a matsayin Ɗan majalisar dattawa a yanzu ya ce hukumar NDDC bata biya ‘yan kwangilar da suka gina hanyoyin da ya gudanar ba.

Kalu a wani jawabi dauke da sa hannun Barista Emeka Nwala ya ce maganar da ke kasa a yanzu a hakumar NDDC shine batu batar kudade ba wai na ayyukan da aka yi ba.

Ya yi bayanin cewa ayyukan hanyar da ministan ya ambata sun kasance na shiga tsakani da shi ya yi domin al’umma a lokacin yana mai zaman kansa kafin zama sanata.

Ya ce an ambaci sunansa ne saboda ya yi amfani da takarda mai dauke da sunansa wajen rubuta wasikar tausayawa zuwa ga hukumar NDDC a 2016, inda ya roki hukumar da ta ceto hanyoyi a Abia.

“NDDC a yayinda suka duba hakan wanda na gode ma hakan, sun bayar da ayyukan hanyoyi ga kamfanonin da suka nemi kwangiloli amma ba wai ni suka baiwa ba. Nasabar da ke tsakanina da aikin shine saboda an aiwatar da ita ne sakamakon shiga tsakani da na yi,” in ji Kalu.

A baya mun ji cewa Majalisar Wakilai ta yi barazanar yin karar Akpabio a kotu kan ikirarin da ya yi na cewa kaso mai yawa cikin kwangilolin NDDC, yan majalisan ne aka bawa.

Ministan ya yi wannan ikirarin ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar da aka kafa domin duba kudaden da ake kashewa a hukumar da ake ganin ya wuce hankali.

Labarai Makamanta

Leave a Reply