Badaƙalar EFCC: ‘Yan Daba Sun Afka Ofishin Sirrin Kudin Najeriya

Wasu ‘yan daba ne suka balle ofishin sashen sirrin kudi na Najeriya (NFIU) inda suka ragargaza na’urori masu kwakwalwa da ke dauke da bayanai da takardu masu matukar amfani ga binciken.

Jaridar THISDAY ta gano cewa, wannan ci gaban ne yasa wasu jami’an NFIU suka bayyana gaban kwamitin bincike na Mai shari’a Ayo Salami, inda ake bincikar Magu.

An kira su ne don karin haske game da wasu takardun da suka jibanci wasu kudi da aka zarga an fitar.

Amma kuma jami’an NFIU sun sanar da kwamitin cewa a ka’idar aikinsu, basu yawo da takardu. Jami’an sun shawarci kwamitin da su samesu a ofishinsu a ranar Juma’a da safe don ganin takardun da suke bukata.

Sai dai kuma, kafin isar mambobin kwamitin ofishin a safiyar Juma’a, wasu mutane da ba a sani ba sun balle ofishin inda suka isa kai tsaye dakin da ake adana bayanan a kwamfuyuta suka ragargazasu.

Bayan aukuwar hakan, jaridar THISDAY ta gano cewa, darakta janar na NFIU, Modibbo Hamman-Tukur, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan rahoton aukuwar lamarin.

Wata majiyar ta ce hakan ce ta sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Magu.

A halin yanzu, balle ofishin NFIU shine rufa-rufa babba a kan bincikar Magu da ake yi kuma ana bincike a kan hakan.

A wani labari na daban, wasu daraktocin hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da wasu manyan jami’an hukumar, a ranar Alhamis sun bayyana gaban kwamitin bincike.

Kwamitin binciken ya samu jagorancin Mai shari’a Ayo Salami a kan zargin rashawa da ake wa dakataccen shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Daga cikin wadanda suka bayyana gaban kwamitin akwai sakataren EFCC, Olanipekun Olukoyede.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, an bincikesu na fiye da sa’o’i 12. An gayyacesu ne don su bada abinda suka sani game da wasu zargi da ake wa Magu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply