Badaƙalar EFCC: Osinbajo Ya Rubuta Takardar Ƙorafi

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya rubuta takardar korafi zuwa ofishin babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa (IGP), Muhammad Adamu, domin neman a binciki ma su alakanta shi da karbar kudi daga hannun Ibrahim Magu.

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar, ya na fuskantar tuhumar almundahana da barnatar da kudade da kadarorin da EFCC ta kwace.

Wata kafar yada labarai ta yanar gizo, PointBlank, mallakar Jack Ude, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta wallafa rahoton cewa Magu ya barnatar da biliyan N39 tare da bawa Osinbajo biliyan N4 daga cikin kudin a matsayin toshiyar baki.

Rahoton ya yi ikirarin cewa wata majiya ce daga cikin kwamitin binciken Magu ta sanar da jaridar labarin bawa Osinbajo kudin.

“Magu ya sanar da kwamitin bincike cewa ya bawa mataimakin shugaban kasa biliyan N4 bisa umarnin shugaban kasa a ranar da zai bar Najeriya zuwa kasar Ingila domin zaman jinya,” a cewar wani bangare na rahoton jaridar Pointblank.

Sai dai, rahoton jaridar bai bayar da cikakken bayani a kan yayin wacce tafiya ne shugaba Buhari ya bayar da umarnin ba, saboda shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila domin a duba lafiyarsa fiye da sau daya.

A cikin wasikar da Osinbajo ya rubutawa IGP ranar Laraba ta hannun lauyansa, Taiwo Osipitan, ya bayyana rahoton a matsayin kage da sharri domin bata ma sa suna, a saboda haka ya bukaci a bi ma sa hakkinsa.

Kazalika, Osinbajo ya aka kwafin wasikar zuwa ofishin ministan shari’a, Abubakar Malami.

Laolu Akande, kakakin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce babu kamshin gaskiya a cikin wasu rahotanni da ke ikirarin cewa maigidansa ya karbi biliyan N4 daga hannun Ibrahim Magu.

A cikin wani jawabi da Akande ya aikewa manema labarai ya bayyana wadancan rahotanni a matsayin na ‘kanzon kurege’ da babu gaskiya a cikinsu.

“Ya kamata mu sanar da jama’a cewa babu gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa, mu na da sahihan bayanai a hannunmu, kawai ana son kawo rudani ne ga kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu.

“Mun san da cewa ana amfani da wasu kafafen yada labarai da ake biya domin cin mutunci ko bata sunan wasu mutane ko kuma don kawai a haifar da rudani a tsakanin jama’ar Najeriya,” a cewar Akande.

Akande ya bayyana cewa babu wani batanci da zai dauke hankalin Osinbajo daga gudanar da aiyukansa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply