Badaƙalar EFCC: Osinbajo Ya Nesanta Kanshi Daga Amsar Biliyan 4 A Hannun Magu

Kakakin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya ce babu kamshin gaskiya a cikin wasu rahotanni da ke ikirarin cewa maigidansa ya karbi biliyan N4 daga hannun Ibrahim Magu.

Wasu kafafen yada labarai sun wallafa cewa Magu, dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, ya sanar da kwamitin bincike cewa ya bawa mataimakin shugaban kasa biliyan N4 daga kudaden da aka kwace a hannun mabarnata.

A cewar rahotannin, Magu ya sanar da kwamitin cewa ya bawa Osinbajo kudin ne bayan ya nemi a sakar ma sa wani bangare na kudaden da EFCC ta kwace. Sai dai, a cikin wani jawabi da Akande ya aikewa manema labarai ya bayyana wadancan rahotanni a matsayin na ‘kanzon kurege’ da babu gaskiya a cikinsu.

“Ya kamata mu sanar da jama’a cewa babu gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa, mu na da sahihan bayanai a hannunmu, kawai ana son kawo rudani ne ga kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu.

“Mun san da cewa ana amfani da wasu kafafen yada labarai da ake biya domin cin mutunci ko bata sunan wasu mutane ko kuma don kawai a haifar da rudani a tsakanin jama’ar Najeriya,” a cewar Akande.

Akande ya bayyana cewa babu wani batanci da zai dauke hankalin Osinbajo daga gudanar da aiyukansa.

A cewar Akande; “tuni ofishin mataimakin shugaban kasa ya mika sunayen kafafen yada labaran da suka wallafa rahoton zuwa hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike da kuma daukan mataki.”

A hannu guda Jam’iyyar PDP ta bukaci a gurfanar da Magu a gaban kotu domin tuhumarsa da aikata almundahana.

PDP ta bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da sakatarenta na watsa labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Laraba a Abuja. A cewar PDP, ta bukaci a gurfanar da Magu ne bayan nazarin dalilan da su ka sa har shugaban kasa ya kafa kwamitin bincike a kansa.

Jam’iyyar ta bayyana cewa binciken da ake gudanarwa a kan Magu ya tabbatar da zargin da ta dade ta na yi a kan cewa hukumar EFCC ta na rufawa jami’an gwamnati mai ci asiri tare da tozarta mambobin jam’iyyun adawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply