Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Badaƙalar EFCC: Na Amince A Gudanar Da Bincike A Kaina – Osinbajo

Mataimakin shugaban Nijeriya farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar da ya kaddamar da bincike kan zargin da ake yi masa na karbar kudade daga tsohon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC Ibrahim Magu.

Lauyan Osinbajo, Taiwo Osipitan ya bayyana zargin a matsayin yarfe da yunkurin bata wa mataimakin shugaban kasar suna, kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka rawaito.

Tuni wannan zargi ya mamaye Najeriya tun bayan tube Magu daga kujerarsa wanda kuma aka kaddamar da bincike kan ayyukansa.

Wata kafar yada labaran intanet da ake kira PointBlank News da Jackson Ude, tsohon daraktan ayyuka na musamman a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ke wallafawa, ta ce Ibrahim Magu ya salwantar da Naira biliyan 39 daga cikin kudaden da hukumar ta kwato daga barayin gwamnati, kuma daga cikin kudaden ya bai wa Osinbajo Naira biliyan 4.

Exit mobile version