Badaƙalar EFCC: Magu Ya Fice Daga Komar ‘Yan Sanda

Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu, ya yi magana a kan radadin da ya ji yayinda aka tsare shi.

Magu ya bukaci ‘yan Najeriya kada su yanke kauna da yaki da rashawa da ake faman yi a ƙasar ƙarƙashin jagorancin hukumar ta EFCC.

Ya ce imma yana a matsayin shugaban EFCC ko akasin haka, “ya zama dole ‘yan Najeriya su rungumi yaki da rashawa, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajirce domin kawar da shi.”

Tsohon shugaban na EFCC ya ce abin da ya fuskanta na “daya daga cikin hadarurrukan da ke tattare da aikin.”

Ya ce dukkanin zarge-zargen da ke yawo duk don a bata sunansa da na EFCC ne.

Magu, wanda ya yi magana hirar da ya yi ta musamman da jaridar The Nation ya ce: “Ta bangarena, zan yi yaki da rashawa har abada. Ina kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan yaki da rashawa.

“Kada su karaya a yakin saboda rashawa na kashe kasa fiye da dukkanin wani abu.

“Ba yakin son zuciya bane. Imma Ina a matsayin shugaban EFCC ko akasin haka, dole a ci gaba da yakar rashawa.

“Abunda na fuskanta ya kasance lamari na “kura ta ci kura” amma Ina kallonsa a matsayin daya daga cikin hadarurrukan da ke tattare da aiki. Amma kada mu karaya.

Kan zargin da ake masa, ya ce: “Duk zancen banza ne. Tarin zarge-zarge ne kawai domin bata mani suna da EFCC. Ban saci kudi ko karkatar da kudi don amfanin kaina ba. Na karanta zarge-zargen kuma na shiga juyayi.

“Ina godiya ga ‘yan Najeriya a kan goyon bayansu, kada su karaya. Ina farin ciki da dawowa, na yi imani za a yi nasara a yaki da rashawa.”

A ranar Laraba, 15 ga watan Yuli ne dai aka saki Ibrahim Magu, kamar yadda rahotanni suka nuna, an saki Magu ne da yammacin ranar bayan ya shafe kwanaki 10 a tsare.

Wannan shine mako na biyu da fara binciken Magu bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari’a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa

Labarai Makamanta

Leave a Reply