Badaƙalar EFCC Da NDDC: Waɗanda Na Amince Da Su Sun Ci Amanata – Buhari

A ranar Juma’a a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari a karon farko ya yi magana a kan zargin cin rashawa da ake zargin wasu shugabannin cibiyoyin gwamnatin tarayya da hukumomi. Wadannan hukumomin sun hada da hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kuma hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta.

Shugaban kasar wanda ya yi jawabin bayan kammala sallar idi a gaban fadar shugaban kasa, ya ce wasu manyan masu mukami na gwamnati a karkashin mulkinsa da wanda ya gabata sun ci amanarsa.

Ya nuna jin dadinsa da yawa aka samo wasu kadarorin kasar nan da aka sace kuma aka siyar, amma yanzu an saka su a tsarin asusu na bai daya (TSA), wanda ba zai yuwa mahandama su taba ba.

“Akwai cin amana da wasu wadanda na yarda da su na gwamnatina da wacce ta shude suke yi”.

An samo wasu kadarori da wasu kudade. “Amma mun kirkiro tsarin asusun bai daya (TSA), wanda dukkan kudin da aka samo ake zubawa ta yadda za a dinga zuba shi babu mai iya taba wa.”

Yayin tabbatar wa da dukkan wadanda ake bincika na da da na yanzu cewa za a ci gaba, ya ce: “Wannan ne yasa muke tsananta bincikar dukkan hukumomin.” Ya jaddada cewa dukkan wadanda ake zargin za a bankadosu kuma za a hukunta su, wanda gwamnatinsa ne za ta yi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, majalisar dattawa da ta wakilai na bincikar kwamitin rikon kwarya na hukumar kula da yankin Neja Delta a kan watanda da wasoso da suka yi da N40 biliyan na hukumar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply