Tsohon Mukaddashin Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, ya karyata rahotannin da ke cewa ya baiwa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, kudi N4bn.
Ya karyata rahoton ne yayinda ya gurfana gaban kwamitin bincike da fadar shugaban kasa ta shirya karo na hudu ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, 2020.
Majiyar Muryar ‘yanci ta ruwaito Magu na cewa ko kadan bai fadawa kwamitin ya ba mataimakin shugaban kasa naira biliyan hudu ba.
” Ya ce ta ina zai samu irin wadannan kudaden da zai iya baiwa wani? Kawai ana son bata masa suna ne.
Magu yace: “Ban fadawa kwamitin cewa na ba mataimakin shugaban kasa N4 billion ba.”
“Ko kadan ba’a ambaci sunan mataimakin shugaban kasa a tattaunawar kwamitin binciken ba. Kuma tunda ba’a ambaceshi ba, ta yaya zan yi maganar cewa na bashi N4bn.”
“Bani da iko kan irin wadannan kudaden, ban bada umurnin baiwa mataimakin shugaban kasa ko wani N4 billion ba.”