Badaƙalar EFCC: An Yi Wa Ofishin Magu Binciken Ƙwaƙwaf

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, aka tura wasu masu bincike da su ka su ka tsefe ofishin shugaban hukumar EFCC da aka dakatar watau Ibrahim Magu.

Rahotanni sunce an lalube ofishin Ibrahim Magu ne a sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami ya ke yi a kan tsohon shugaban hukumar na EFCC. Rahotan ya fahimci cewa an dauki wata na’ura mai kwakwalwa daga ofishin shugaban hukumar.

Ana tunanin za a samu muhimman bayanai a cikin wannan gafaka. Bayan haka kuma masu binciken sun taso wasu manyan jami’an EFCC a gaba da tambayoyi jiya.

Masu binciken sun lalube ofishin, sannan su ka tafi da wata babbar gafaka da ake zargin akwai bayanai a cikinta.” “An bukaci wasu manyan mukarraban Magu su bayyana a gaban kwamitin binciken domin su yi wasu karin bayani. Su na wurin har kusan karfe 9:30 na dare.”

Bayan an lalube ofishin na Magu, an kuma tsare wasu manyan hadimansa. Jaridar ta The Nation ta ce an yi wa mukarraban tsohon shugaban hukumar tambayoyi a jiya. Daga cikin wadanda aka rutsa a binciken akwai wani mukaddashin darektan harkokin karbe dukiyar sata na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon-kasa.

An karbe wayoyin wasu daga cikin wadannan hadimai inda aka binciki wasu bayanai. A karshe an kyale su sun tafi gida bayan dare ya tsala.

Ana tunanin cewa kwamitin ya na neman karin bayani ne a game da wasu kadarori 332 da hukumar EFCC ta karbe daga hannun barayi a karkashin Ibrahim Magu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply