Badaƙalar EFCC: An Hana Magu Gabatar Da Takardar Kare Kai – Lauya

Tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da lauyansa Wahab Shittu a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli sun so gabatar da wata takarda mai dauke da shafuka 34 gaban kwamitin bincike, Takardun na dauke da hujjojin kariya ga Ibrahim Magu, sai dai rahotanni sun bayyana cewa an hanasu gabatar da hujjojin gaban kwamitin fadar shugaban kasar.

Mun ruwaito maku cewa Magu da lauyansa sun bayyana gaban kwamitin binciken dake karkashin mai shari’a Ayo Salami da misalin karfe 1 na rana har zuwa karfe 6 na yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa ya isa fadar shugaban kasar tare da lauyansa Shittu da kuma wasu hadimansa. Sai dai an ruwaito cewa Magu da Shittu ne kawai aka bari suka shiga cikin babban dakin gudanar da binciken, inda suka zauna na tsawon awanni.

Kundin hujjojin mai dauke da shafuka 34, ya kunshi hujjoji a rubuce, da hotuna, an kawo shi ne da nufin gamsar da kwamitin cewa duk tuhumar da ake yiwa Magu karya ce tsagoronta.

Jaridar Vanguard ta yi nuni da cewa lauyansa, Shittu, a wayar tarho ya ce ba a bari suka gabatar da wannan kundi ba a ranar (Alhamis). “Amma dai zamu koma yau (Juma’a),” a cewar lauyan, duk da cewa bai bayyana dalilin da ya sa aka hanasu gabatar da hujjojin ba.

Kwamitin fadar shugaban kasar na tuhumar Magu akan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun wadanda suka saci kudin jama’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply