Jam’iyyar PDP tace zaiyi wahala kwamatin dake bincikar dakataccen shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu basu dawo dashi bakin aikinsa ba duk da tuhumar da ake masa, wannan babban abun kunyane ga shugaban kwamatin binciken da shugaban kasa Buhari ya kafa domin duba ayyukan hukumar ta EFCC.
Jam’iyyar tace ta kadu sosai da ita da sauran yan Najeriya da sauran da aka dakatar , Wahab Shittu, wanda har yanzu ba’ayiwa mutane bayani ba akan alakarsa da Magu ba , amma daga baya aka mai dashi ofis.
Yan Najeriya sunyi mamaki lokacin da lauyan Magu yake bayyana wannan batu akan shugaban kwamatin binciken da kuma fadar shugaban kasa Buhari inda suke kokarin sauya wannan zargin.
Jam’iyyarmu tana fatan wannan dambarwar bazata dawo da hannun agogo baya ba akan yaki da cin hanci da ake ba a kasar nan.
Dadin dawa, wannan bayanan da lauyan Magu yayi ya nuna cewa zaiyi wahala ba’ayi watsi da wannan zargin da akewa Magu ba duk da kiran da yan Najeriya suke na a tabbatar an mika dakataccen shugaban EFCC din zuwa kotu.
PDP tace zata yanzu yan Najeriya sun fara tunanin ko dai an kirkiri wannan dambarwar ne tun daga kan su yan kwamatin da shugaban kasa ya kafa da kuma wasikar da ministan shari’a ya rubuta ko dai duk an kirkiresune don kawai a wanke Magu a idon yan majalisaar dattawa .
Jam’iyyar tace yan kasar nan bazasu manta da zargin da ministan shari’a ya rubuta akan Magu, musamman kan yanda aka sace kudaden hukumar ta EFCC , sace kudaden da aka dawo dasu, da kuma kudaden da aka sai kadarorin hukumar EFCC, da kuma saura zargi masu yawa dake kansa , da sauransu.
Da kuma zargin karya dokoki, da karya dokikn kotu wajen wadanda ake zargi, karya dokokin kotu duk a karkashin Magu, da kuma cin mutunci da tozarta yan Najeriyar da basuji basu gani ba.
Akwai zargin da akewa wannan hukumar ta EFCC a karkashin Magu wajen tauye hakki maimakon tabbatar da adalci; inda wanda basuji basu gani ba ake kamasu a daure akan zargin karya, a hana belinsu, da rubuta bayanan karya akansu batare da amincewar lauyoyinsu ba duk suna tsare a dunga watsawa a sabbun kafafen yada labarai ba tare da an kaisa kotu ya kare kansa.
Dadin dawa, akwai hujjojin dake bayyana yanda wannnan hukumar ta EFCC ta sha tursasa alakalai suna yanke hukuncin dabai dace ba , da kuma zabar wanda za’a kama a daure duk a wannan gwabnatin , kuma an bar wanda ya kamata a kama saboda sata, anje ana daure wanda basuji ba a EFCC.
Wannan bayanin na Magu, ya tabbatar da rashin gaskiya da ya kuma kunyata bangaran shari’a da kuma karyar yaki da cin hancin da ake a Najeriya .
Abun da yan Najeriya suke fatan ji daga wannan gwabnatin tarayya da shugaban kasa Muhammad Buhari ke jagoranta kuma matsayin jagoran yaki da cin hanci na Afrika da (AU) ta kafa dasu gaggauta mika tsohon dakataccen hukumar ta EFCC dasu gaggauta mikasa kotu domin ya kare kansa akan zargin da ake masa.
Duk wani abu sabanin haka yan kasar nan bazasu amince da shi ba.
Sa hannu
Kola Ologbondiyan
Sakataren watsa labarai