Gwamnatin kasar Ireland ta sanya hannu kan takardar yarjejeniya da gwamnatin Najeriya don dawo da wasu makudan kudi da tsohon shugaban kasan mulkin Soja, marigayi Janar Sani Abacha, ya boye a kasar €5.5m da yake daidai (N2bn).
Ma’aikatar shari’a da daidaito ta kasar Ireland ta bayyana hakan ranar Alhamis, Kudin na cikin $5billion da tsohon shugaban kasan ya wawura tsakanin 1993 da 1998 da yayi mulki.
Ministar shari’ar kasar Ireland, Helen McEntee, tace, “Ina matukar farin ciki akan sanya hannu kan wannan takardan yarjejeniyar tsakanin Ireland da Najeriya.” “Wannan shine sakamakon binciken da aka kaddamar na lokaci mai tsawo.”
“Hukumar yaƙi da dukiyoyin haram ta taka rawar gani a wannan bincike na duniya inda aka samu damar daskarar da kudi $1bn a fadin duniya, kuma €5.5 million ciki na cikin wani asusun banki a Dublin.” “Hukumar ta daskarar da Kudaden da tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, ya wawura ne a wani banki kasar Ireland a Oktoban 2014.”
“Bayan gwamnatin kasar Najeriya ta bukaci kudin shekarar da ya gabata, babbar kotu ta bada daman mayar da kudaden Najeriya.” A cewar ministar, mayar da wadannan kudaden shine karo na farko da kasar Ireland zata yi irin wannan kuma hakan na nuna cewa tana hada kai da duniya wajen yaki da rashawa da taimakawa kasashen da rashawa ya nakasa.
A watan Febarairu 2020, Gwamnatin Najeriya, gwamnatin kasar Jersey da gwamnatin kasar Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyar dawo da kudaden da tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha ya jibgesu a kasashen waje.
An ruwaito ofisoshin jakadancin Najeriya da na Amurka ne suka bayyana haka a ranar Litinin, inda suka ce yarjejeniyar ta amince da dawo ma gwamnatin Najeriya kimanin dala miliyan 308 mallakin Abacha.
An tura wadannan kudade ne ta bankunan kasar Amurka, inda aka jibgesu a asusun bankin kasar Jersey da sunan wani kamfani Doraville Properties Corporation, wanda yaron Abacha ke shugabanta.