Wata sanarwa da Minista Ya?a Labarai Mohammed Idris ya fitar ta ce wannan batu “ba shi da tushe” kuma “gwamnatin tarayya ?ar?ashin mulkin Bola Tinubu ba ta yin wata tattaunawa da kowace ?asa game da hakan”.
A ?arshen makon da ya gabata ne wasu cibiyoyi da manyan mutane a arewacin Najeriya suka rubuta wa gwamnatin wasi?a suna garga?in kada a bai wa ?asashen damar kafa sansanin soji a Najeriya, bayan korar su da aka yi daga wasu ?asashen yankin Sahel.
“Muna neman jama’a su yi watsi da wannan ?aryar,” a cewar sanarwar.
“Ba mu samu wata bu?ata ko tattaunawa da wata ?asa ba kan wannan batu game da kafa sansanin wata ?asar waje a Najeriya. Da ma tuni Najeriya na ci gaba da amfana daga aikin ha?in gwiwa wajen da?ile matsalolin tsaro.”
Tuni ?asashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka fatattaki sojojin Faransa da na Amurka daga ?asashensu kuma suka gayyaci na Rash