Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Babu Wata Makarkashiya Da Ake Yi Wa Matatar Man Dangote- Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Najeriya ta fara yun?urin sasanta rikicin sa?anin da aka samu tsakanin matatar mai ta Dangote da kuma hukumomin da ke kula da harkokin man a ?asar.

?aramin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce ya jagoranci wani zama da Aliko Dangote shugaban kamfanin Dangote, da Mele Kyari shugaban kamfanin NNPCL, da Farouk Ahmed shugaban hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), da Gbenga Komolafe shugaban Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC) a yammacin yau Litinin.

“Ganawar wani yun?uri ne na gano maganin matsalolin da matatar ke fuskanta,” in ji ministan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

“Dukkan ?angarorin sun nuna aniyarsu ta nemo bakin zaren kuma sun nuna jin da?insu da yun?urin sasantawar da ake yi.”

Wannan ne karon farko da ?angaren gwamnati ya yi magana kan cecekucen da ?angarorin ke yi bayan hukumomin sun zargi matatar Dangote da fitar da man dizel maras inganci, wanda ta musanta ta hanyar gudanar da gwaji a gaba ‘yanmajalisar tarayya ranar Asabar.

Aliko ya koka kan yadda kamfanonin cikin gida suke ?in sayar wa matatar tasa ?anyen man fetur ?in domin fara tace shi da kuma sayar da shi a Najeriya.

Exit mobile version