Babu Wata Karuwa Ko Dan Daudu Da Za Su Sarara A Kano – Daurawa

FB IMG 1709460172709

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Shugaban Hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya lissafa abubuwa 3 da za su yi a inganta aikinsu a Kano Bayan ban hakuri da zaman sulhu, Daurawa ya ba ‘yan daudu da karuwai wa’adin barin Kano

Sai dai kuma, yayin da wasu ke ganin abubuwan da suka faru a baya za su kawo cikas ga ayyukan Hisbah, Shehin malamin ya ce hakan karfafa masu gwiwar kara kaimi kan ayyukansu ya yi.

Daurawa ya kuma ce sun ba duk wasu masu yada badala, kama daga ‘yan daudu zuwa mata masu zaman kansu makonni biyu su tuba, sannan cewa za a basu kudi domin su ja jari tare da koya masu sana’a.

A wata hira da aka yi da shi, malamin ya gargadi wadanda ba su da niyyar tuba da su tattara su bar Kano domin jihar ba ta fasikai bace.

A hirarsa da sashin Hausa na BBC, malamin ya ce: “Yanzu ai kara karfafawa aka yi, yanzu babu wani takunkumi, dari bisa dari babu wani sharadi da aka yi cewa za mu mayar da aikinmu baya face ma an ce za a karfafa mana gwiwa ne don aiki ya ci gaba fiye da da.

“Don haka ne yanzu wani abu da ya faru kamar ma ya bazawa abin taki ne, don haka wadanda suke ganin ‘yan daudu ne da karuwai da fasikai hukumar Hisbah ta basu sati biyu wanda yake so zai tuba.

“Akwai fam da muka buga sunansa na tuba za a ba mutum ya je ya cika, za a ba mutum jari, za a koya masa sana’a, za a mayar da shi garinsu idan ba ‘dan Kano ba ne. “Wanda kuma bai tuba ba, ba kuma zai bi dokoki ba zai ci gaba da karya doka toh lallai gara ya tattara kayansa ya kara gaba, Kano ba matattarar badala bace.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply