Babu Wani Cigaba Da Gwamnatin Buhari Ta Samu – Bishop Kukah

Labarin da muke samu daga Jíhar Sokoto na bayyana cewar Babban Bishop na Cocin Sokoto Bishop Matthew Hassan-Kukah ya ce duk da irin manyan alkawura da dama da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, a yanzu zai bar ‘yan Najeriya “a matsanancin talauci” fiye da lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu, 2015.

Fitaccen malamin addinin ya kara da cewa baya ko tantama lafiyar Buhari ta karu a tsawon shekaru bakwai da rabi da suka shude amma yaso a ce miliyoyin ‘yan Najeriya sun mori tagomashi daga ingantacciyar lafiyar da Buhari ya samu ta hanya damar samun ingantacciyar kulawa ta lafiya a kasar.

Bishop Kukah ya fadi hakan ne a sakon Kirsimetinsa na shekarar 2022, mai taken, ‘Najeriya: Bari mu bude sabon shafi’ wanda ya gabatarwa Daraktan sadarwa na Channels TV, Rabaran Christopher Omotosho.

“Mai girma shugaban kasa, ina taya ka da iyalinka murnar Kirsimeti. Ina magana ne a madadi na da sauran ‘yan Najeriya idan nace, mun gode Ubangiji da jinkansa ya baka ingantacciyar lafiya.

“Mun sani cewa a yanzu kafi lafiya fiye da yadda kake a da. Muna ganin hakan ne da takunka, nisan tafiyar da kake ci gaba da yi kasashen ketare. Ubangiji ya karo maka shekaru cikin koshin lafiya.

“Sai dai, Ina fatan miliyoyin ‘yan kasa sun samu damar morar wani bangaren daga cikin lafiyarka ta hanyar samun cigaba wajen inganta asibitocin kasarmu. “Abun takaici shi ne, duk da irin tarin manyan alkawuran da ka yi, zaka bar mu cikin matsanancin talaucin da yafi na baya da kazo ka same mu a ciki, wannan rashawar da muka yi zaton za a kawo karshenta ta zama ruwan dare.

“A sakona na Kirsimetin shekarar da ta gabata, na nuna yadda tayi wa dokar kasa hawan ‘kawara ta hanyar ragewa wajen girmama da bin dokokin dokar tarayya. Dukkanmu shaidu ne.”

A hannu guda yayi jinjina ga shugaban kasa bisa kokarin da yayi a bangaren kayan masarufi sannan yana kokarin kawo karshen magudi a bangaren zabe.

“Kana ganin zan yarda ka sani amma ba kayi komai ba game da tikitin musulmi da musulmi a jam’iyyarka? Duk da haka, muna fatan zaben mara magudi.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply