Babu Wanda Ya Kamu Da Cutar Anthrax A Najeriya -NCDC

Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce har yanzu cutar Anthrax – da wasu dabbobin ƙasar ke fama da ita – ba ta yaɗu zuwa ga bil-adama ba.

gidan Talbijin na ƙasar NTA ya ambato shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed na cewa hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ɓulla a ƙasar.

Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin ma’aikatar lafiyar ƙasar na ƙarfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ɗaukar ta, musamman a masarautar Suleja da ke jihar Naija.

Sarkin Suleja Muhammadu Auwal Ibrahim ya yi kira da hakiman masarautar da su kai rahoton rashin lafiyar dabbobi a yankunansu, tare da kauce wa cin naman da likitocin dabbobi ba su tantace lafiyarsa ba.

Tuni dai gwamnatin ƙasar ta bayyana sayen alluran riga-kafin cutar domin yi wa dabbobi a garin Suleja, inda cutar ta fara ɓulla.

Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ɗauke da ita.

Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.

Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply