Babu Wanda Ya Isa Ya Kori Kukah Daga Sokoto – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan bukatar da wata kungiyar Musulmai a Sokoto ta yiwa Bishop Matthew Kukah cewa ya janye maganar da yayi ko kuma ya tattara inasa-inasa daga jihar Sokoto cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace wannan ba daidai bane kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya gaba ɗaya.

Garba Shehu ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar da yammacin ranar Laraba mai taken, “Wajibi ne a rabu da Bishop Kukah yayi addininsa da siyasarsa.”

“Rahoton da wata kungiya a Sokoto mai suna ‘Kungiyar hadin kan Musulmai,’ wacce ke kira ga Bishop na cocin Sokoto, Rabaran Matthew Kukah ya baiwa al’ummar Musulmai hakuri kan jawabinsa kan Musulunci ko ya fita daga jihar.” “Wannan ba daidai bane kuma ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.”

“Karkashin kundin tsarin mulkinmu, kowane dan Najeriya na da hakkin fadin abin da ya ga dama, ya mallaki abinda ya ga dama, kuma ya zauna duk inda ya ga dama a kasar nan ba tare da tsangwama ba.”

CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto Mun kawo muku cewa babban faston darikar Katolika a kasar Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya na fuskantar barazana bayan jawabinsa da ya yi na bikin kiremeti a 2020.

Ƙungiyar al’ummar Muslimi ta bukaci Faston ya fito ya bada hakuri game da kalaman da ya yi, ta ce idan ba haka ba, ya yi gaggawa ya bar jihar Sokoto salin-alin.

Labarai Makamanta