Babu Wanda Ya Isa Ya Hanamu Albashi – Malaman Jami’o’i

A ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoba, 2020, Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce malamai sun shirya kare martabar Jami’o’i, akan biyan albashi.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa a shirye ASUU ta ke ta takawa gwamnatin tarayya burki na yunkurin murkushe jami’o’i da ta ke yawan yi, babu gaira babu dalili.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, ya yi wannan jawabi ne a garin Ibadan, ya na mai maida martani ga jawabin da Shugaban kasa Buhari ya yi, na cewar ba za’a biya malamin jami’ar da bai yi rijista da IPPIS albashi ba.

Farfesan ya tunawa shugaban kasar cewa ana bada wannan umarni ne ga sauran ma’aikatan gwamnati gama-gari amma ba malaman jami’o’i ba, domin malaman jami’a a sahu dabam su ke.

Ƙungiyar ASUU ta ce ta yi magana da shugaban kasa a Janairun 2020, inda su ka fahimci juna cewa za su kirkiri manhajar UTAS da za a rika biyansu albashi. Ogunyemi ya ce babu dalilin da zai sa Muhammadu Buhari ya yi maganar da ya yi, bayan ya amince su kirkiri manhajar da za ta yi aiki a kan malamai.

A cewarsa sun gabatar da manhajar a ma’aikatar kudi, kuma su na jira su nunawa ma’aikatar tattalin arziki aikin da su ka yi bayan sun kashe miliyoyin kuɗi.

A dalilin haka ne Farfesa Ogunyemi ya ce shugaban kasa bai isa ya ce ba zai biya malamai ba. Kuma wannan shirin da aka kawo ya taba martabar jami’o’in kasar nan.

An ruwaito Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan majalisa cewa ma’aikatan gwamnatin da ba su cikin manhajar IPPIS ba su da rabo a kasafin kudin kasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply