Babu Sauran ‘Yan Boko Haram A Arewa Maso Gabas – Buratai

Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa jami’ansa sun fatattaki ‘yan ta’addan Boko Haram daga dukkan jihohin Arewa maso gabas face jihar Borno, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ganawar sa da shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2020.

Hafsan Sojan, ya kara da cewa yanzu haka jami’ansa na amfani da labaran leken asiri domin kawar da yan ta’addan daga Borno.

Babu yan Boko Haram a sauran jihohin dake makwabtaka. An fitittikesu, yanzu suna boye a jihar Borno.

Muna aiki tare da masu fararen hula da sarakunan gargajiya, abinda muke bukata kawai shine hakuri. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba.” ya bayyana a jawabin da kakakin Buhari, Garba Shehu ya fada.

Duk da wannan ikirari da Buratai ke yi, a watan Mayun nan yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Dapchi, a jihar Yobe. Gabanin nan ma sun kai wani garin Babangida a jihar awatan Febrairu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply