Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) Biodun Ogunyemi, ya ce ‘ya’yan kungiyar da yake wakilta ba za su koma bakin aiki ba har sai an biya musu bukatunsu.
A cewarsa “ASUU” ba ta da alhakin rufe makarantu. Don haka, gwamnati ta yi abin da ta san yadda za’a yi mafi kyau, wanda yake shi ne bayarwa da bibiya kan umarnin, kamar yadda ya fada wa TheCable
“Game da ASUU, ba a biya bukatun kungiyarmu ba.”
Ya bayyana cewa ana sa ran kungiyar kwadagon za ta gana da gwamnatin tarayya a ranar 17 ga watan Satumba, amma kungiyar ta janye daga shirin a kan cewa ba ta shirya ba tukuna.
Ogunyemi ya ce aikin ASUU na game da yajin aikin da ke gudana za a tantance shi ne ta hanyar taron.
Ya kara da cewa kungiyar kwadagon tana jiran gwamnatin tarayya ta sanar da sabuwar ranar da za a yi taron.
Kungiyar a watan Maris ta ayyana yajin aiki na ba-sani-ba-sabo, saboda gazawar gwamnatin tarayya na biyan bukatun ta.
Matakin masana’antar ya kasance a bayan rashin jituwa da gwamnati kan batutuwan da suka shafi farfado da jami’o’in da kuma samun alawus na ilimi.
Sauran batutuwan da kungiyar kwadagon ta gabatar sun hada da Hadakar Albashi da Tsarin Bayanan Ma’aikata (IPPIS) gami da tallafin jami’oi.
Ministan ilimi Adamu Adamu ya sanar da cewa za a bude makarantu a ranar 12 ga watan Oktoba.
Ya kara da cewa makarantu masu zaman kansu da na jihohi za su tantance jadawalin yadda za su bude amma ya yi gargadin cewa dole ne su tabbatar da bin ka’idojin COVID-19 sosai.