Babu Ranar Janye Yajin Aiki – Ƙungiyar Malaman Jami’o’i

Kungiyar Malaman jami’o’i ta yi watsi da jita-jitan da ke yawo a kafofin ra’ayi da sada zumunta cewa ‘ya’yan Ƙungiyar sun janye daga yajin aikin da suka tafi tun watan Maris.

Kungiyar ta yi tsokacin haka ne ta shafinta na Tuwita yayinda matasa a Tuwita suke tafka muhawara kan janye yajin aikin.

A cewar kungiyar, rahoton karya ne, na bogi ne, kuma babu kamshin gaskiya ciki.
“Sabanin rade-radin dake yawo a kafafen ra’ayi da sada zumunta cewa kungiyar Malaman jami’a ASSU sun janye yajin aikin, babu gaskiya cikin haka.” “Idan zamu janye yajin aiki, akwai matakai da ake bi kuma har yanzu bamu bi matakan ba.”

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemu, ya lashi takobin cewa kungiyar ba zata gushe tana yaji ba har sai gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatunta.

Ogunyemi ya ce ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar 2012 da akayi.. Ya kara da cewa abin takaici ne ace tun shekarar 2009 malaman jami’a basu samu sauyin albashi ba.

Ya jaddada cewa wajibi ne a duba lamarin kafin ASUU ta janye wannan yajin aikin. A cewarsa, “Ga matsalan albashi; ba’a magance ba. Da alamun akwai wasu kusoshi a gwamnati da suka rantse sai ‘ya’yan kungiyarmu sun wahala ta hanyar rike musu albashi.”

Malaman Jami’a sun shiga yajin aiki gab da bulluwar cutar Korona a wata Maris. Tun daga lokacin daliban jami’o’in gwamnati dake kasar gaba daya suke zaune a gida.

Labarai Makamanta

Leave a Reply