Shugaban Kungiyar Gamayyar Matan Jihar Katsina, Hajia Nana Mustapha ta bayyana cewa a halin yanzu a jihar Katsina, babu macen da gwamnatin Aminu Bello Masari da matakin tarayya da ba’a tallafa mawa ba ko dai ta fuskar ba da tallafi ko kuma koya masu sana’o’in hannu, domin su zama masu dogara da kan su. A jihar Katsina a halin yanzu babu mace da ke zaune ba ta da sana’a ko jari wanda gwamnatin APC ta bada ba, a lungu da sakon jihar Katsina.
Hajia Nana Mustapha ta bayyana haka a lokacin da take jawabin godiya a madadin wadanda suka amfana da tallafin da Sanata Kabir Abdullahi Barkiya ya raba wa al’umma mazabarsa ta Katsina ta tsakiya a wajen taron (People’s Square) da ke kallon gidan Gwamnatin Jihar Katsina yau Asabar.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Mata ta jihar Katsina, ta kara da cewa muna godiya da irin tallafin da Gwamnatin APC ke ba mu tun farkon hawan gwamnati a 2015 kala-kala. Kama ya zuwa keken dinki da injinan markade da janareto da abinci da kuma sutura. Ina da yakinin cewa matsayin da ake a jihar Katsina, ba na tunanin akwai wata diya mace da take zaman banza ko rashin jari. A shekarun baya da wuya ka ga diya mace tana shiga harkokin siyasa, saboda ba’a fahimci muhimmancin ta ba, amma yanzu mazajen na su ke ba su kwarin gwiwa saboda alherin da suke zuwa da su a gidajen auren su.
Hajia Nana ta ci gaba da cewa gwamna Aminu Bello Masari adalin jagora ne, abin koyi, shi yasa masu rike da mukaman siyasa suke koyi da shi wajen tallafa wa al’umma jihar Katsina. Tun farkon hawan su ake kokarin tallafawa al’ummar jihar Katsina kuma har yanzu ba’a fasa. Ayyukan alheran babu mace dake lungu da sakon jihar Katsina ba ta amfana da tallafin ba.