Babu Komai A Mulkin Buhari Sai Tashin Hankali – Gurgun Da Ya Taimaki Buhari

A ‘yan kwanakin nan ana ta yawo da hoton mutumin a sabbin kafafen sadarwa inda al’umma da dama suka dunga bayyana ra’ayoyi game da mutumin har ana cewa ya sha jar miya, a saboda haka ne abokin aikin mu Shuaibu Abdullahi, ya yi tattaki don jin shin kwalliya ta biya kudin Sabulu?

To sai dai Malam Abdullahi Aliyu, mazaunin Jihar Kaduna, ya ce babu wani abun da ya amfana da shi a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, banda tashin hankali, tsadar kayayyakin abinci, gashi ana ta kashe musu ‘yan uwa a jihar Zamfara.

“To ba zan ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba tunda ni dan Allah na baiwa Buhari tallafi, domin Nijeriya da sauran al’umma su sami ci gaba idan aka kafa sabuwar Gwamnati, sai dai ba yadda aka zata ba, domin ana fama da kashe-kashe a sassan Nijeriya”, inji shi.

Malam Abdullahi Aliyu, ya kara da cewar “labari ya karade gari cewar an ba ni manyan kudade, wallahi ni babu wanda ya taimake ni, ban ga kowa ba kuma babu wanda ya aiko mun da sako.

“Wallahi ina neman taimako. Maganar da ake yi ko matsugunni ba ni da shi, rayuwa ta yi mun wuya, babu wanda ya taba taimaka mun tunda aka kafa sabuwar Gwamnati. Don Allah don Annabi a taimake ni”, cewar Malam Abdullahi.

Labarai Makamanta