Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban ƙasa ta fitar da wata sanarwa da ke cewa babu wata jihar da aka ba izinin sayo makaman yaki masu sarrafa kansu domin raba wa kungiyoyinsu na samar da tsaro.
Sanarwar Fadar ta kuma ce ta dade tana nanata cewa babu mutumin da aka ba izinin mallakar bindiga iri samfurin AK-47 ko ma wata bindiga mai sarrafa kanta, inda ta ce tilas ne su mika irin bindigogin ga hukumomin tsaron kasar.
Fadar ta kuma ce an ba jami’an tsaro umarni su hukunta wadanda suka ki bin wannan umarnin.
Mallam Garba Shehu, wanda shi ne mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanya hannu kan wannan sanarwar.
Ya tabo batun Jihar Katsina, wadda ya ce gwamnan jihar ya rubuta wasikar yana bayyana cewa ya gayyaci shugaban kwalejin da ke horar da jami’an Civil Defence da ya tura nasa jami’an Katsina domin su koyar da ‘yan bijilanten jihar yadda ake amfani da bindiga amma ba mai sarrafa kanta ba.
Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’ar kasar da su guji mayar da batun tsaro ya koma tamkar na siyasa.