“Ƙasar Arewa ta shiga cikin wani mawuyacin hali da shekaru 100 baya ba ta shiga irin sa ba, sakamakon yadda tsaro ya taɓarɓare a yankin, ba Birni ba ƙauye, ana kisan jama’a da sace su da aikata fyaɗe da sauran miyagun laifuka waɗanda a baya yankin bai taɓa tunanin gani ba, babu shakka wannan wani iftila’i ne da har abada Arewa ba za ta manta ba”.
Waɗannan Kalamai sun fito ne daga bakin ɗaya daga cikin Dattawan yankin Arewacin Najeriya, Dakta Hakeem Baba Ahmed a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin da rediyo na Liberty Abuja ya yi shi, akan halin rashin tsaro da Arewa ke ciki da kuma hanyar magance matsalar.
Baba Ahmed ya kara da cewa a fili yake shugaban ƙasa Buhari a matakin tarayya ya gaza wajen cika alƙawurran da ya yi wa ‘yan Najeriya na kare rayuka da dukiyoyinsu, al’amurra suka ƙara dagulewa a yankin Arewa ya zamana gwamma jiya da yau.
“A baya can abin da Arewa ke fama da shi shine shine matsalar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas kawai, amma a halin da ake ciki yanzu matsalolin sun nemi nunka na baya, inda bayyanar ‘yan Bindiga da masu garkuwa da mutane suka faɗaɗa a yankin Arewa maso yammacin ƙasar”.
Dangane da kiran da wasu ke yi na cewar a canza Shugabannin tsaron ƙasa domin samun ingantaccen tsaro, Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewar matsayin da kungiyar su ta Dattawan Arewa ta ɗauka shine ba canza Shugabannin tsaron ba ne damuwa, damuwar ita ce ya zama wajibi a yi garambawul a tafiyar da rundunar soji ke akai yanzu, indai zai zamana rundunar Sojin Najeriya ta gagara kawar da Boko Haram tsawon shekaru, to babu shakka da akwai inda gizo ke saƙa.
“Malaman addini sun yi ma wannan gwamnati kamfe a zaɓukan 2015 da na 2019, a yanzu abubuwa sun dagule malaman kuma sun yi shiru, Sarakuna suma sun yi tsit duk da halin koma baya da talauci da Arewa ke ciki.
Dattijon Arewan ya bayyana cewar babu shakka ‘yan Najeriya sun yi zaben tumun dare a shugabannin da suka zaba, saboda haka lokaci ya yi da za’a ɗauki darasi ta hanyar duba cancanta ba harshe ko asalin mutum ba.