Babu Inda Ake Shan Fetur Arha A Duniya Kamar Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa farashin fetur a Najeriya har a yanzu shine mafi karanta a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika.

Ministan ya bayyana hakan a yayin jawabi ga manema labarai na hadin guiwa wanda ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva suka hada.

Mohammed ya ce , duk da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, gwamnati ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukanta ballantana biyan albashi. Amma kuma dole ne ta cire wa kanta al’adun da za su durkusar mata da tattalin arzikinta.
“Gwamnati ba za ta iya bada tallafin man fetur ba saboda bata ganin daidai a hakan. Yawaita neman man fetur yanzu ya zama tarihi.

“Lokutan da ‘yan Najeriya ke daukar tsawon sa’o’i suna jiran layi ya zo kansu ko kwanaki domin siyan man fetur duk ya wuce. “Tabbas ko a kasafin kudin 2020 da aka sake bitarsa babu tallafin man fetur saboda ba za mu iya biya ba,” yace.

Ministan ya bayyana cewa, daga 2006 zuwa 2019, tallafin man fetur kadai ya lashe N10.413 tiriliyan kuma a duk shekara yana lashe N753.8 biliyan.

Ya ce matatar man fetur ta kasa ta bayyana cewa, an fitar da tallafin man fetur har N257 biliyan a 2006, N272 biliyan a 2007, N631 biliyan a 2008, N469 biliyan a 2009, N667 biliyan a 2010, N2.105 tiriliyan a 2011 da N1.355 tiriliyan a 2012.

Ya kara da cewa, tallafin man fetur ya lamushe N1.316 tiriliyan a 2013, N1.217 tiriliyan a 2014, N654 biliyan a 2015, N144.3 biliyan a 2017, N730.86 a 2018 da N595 biliyan a 2019.

Labarai Makamanta

Leave a Reply