Babu Imani A Harin Da Rasha Ta Kai Ukraine Da Makami Mai Linzami – Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kaddamar ranar Litinin zuwa wasu yankuna na Ukraine, sun nuna irin ‘rashin imanin’ Vladimir Putin kan haramtaccen yakin da yake yi a Ukraine.

Yana mai zargin Rasha da kashe tare da raunata fararen hula masu dimbin yawa, ya kara da cewa kasarsa na tare da al’umar Ukraine.

Ya nanata kiran Rasha da ta gaggauta kawo karshen wannan yaki, tare da janye dakarunta daga Ukraine.

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce ya kadu matuka da wannan mataki da Rasha ta dauka.

China da India kuma sun kasance ne yan ba-ruwanmu, inda suka yi kiran a kai zuciya nesa ba tare da sukar Rasha ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply