Babu Gwamnatin Da Za Ta Iya Magance Matsalolin Najeriya – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wata gwamnati da za ta iya magance matsalolin kasar nan baki daya.

Ya ce mafita daya da ake da ita, ita ce gwamnatoci su rika dorawa daga inda na baya suka tsaya.

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a wajen taron tattauna halin da kasa ke ciki wanda Kungiyara Lauyoyi ta Najeriya ta shirya a Abuja.

BBC ta rawaito A cewarsa, “ina iya cewa babu wata gwamnati daya a kasar nan da za ta iya magance matsalolin Najeriya baki daya.

“Amma idan ya zamana gwamnatoci na dorawa daga inda magabata suka tsaya ba tare da shafe ayyukansu ba, za mu cim ma nasara.

“Su dauki matsala daya ko biyu su maida hankali wajen magance su sannan su ci gaba,” in ji Buhari.

Buhari wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya wakilta, ya yi fatan taron ya mika musu duka shawarwarin da ya cim ma domin ba su damar sakawa cikin bayanan da za su tattara yayin mika mulki ga gwamnati mai zuwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply