Babu Gudu Ba Ja Da Baya Sai Karancin Albashi Ya Koma Miliyan Guda – Kungiyar Kwadago

IMG 20240229 WA0092

Shugaban kungiyar ‘yan kwadago watau NLC na ƙasa reshen jihar Ogun, Hammed Ademola-Benco, ya tabo batun karancin albashi.
Hammed Ademola-Benco ya ce ba su canza shawara a kan biyan akalla N1m a kowane wata ba.

A baya kungiyar kwadago tayi zancen cewa ya kamata duk wani ma’aikaci ya rika samun akalla miliyan a matsayin albashinsa.
Shugaban ‘yan kwadagon ya nuna suna nan a kan wannan matsaya, ba za su janye ba yayin da aka gama zanga-zangar lumuna.

‘Dan gwagwarmayar ya bukaci gwamnatin tarayya ta magance matsalolin rashin tsaro, yunwa da tsadar rayuwa da ake ciki. jagoran yana cewa ba za su janye bukatarsu na ganin an tsaida N1m ya zama karancin albashin ma’aikaci ba.

Ademola-Benco yana so daga N38, 000, gwamnati ta nunka mafi karancin albashin kasar duk da ba a biyan hakan a wasu jihohi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply